IQNA

A rika yin taka tsan-tsan  akan batun Ahlul Baiti (AS) 

17:20 - August 27, 2023
Lambar Labari: 3489714
Najaf (IQNA) Da yake amsa tambaya kan Ahlul Baiti (AS), babban malamin addini a kasar Iraki ta bukaci a kaucewa wuce gona da iri a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatullah Sayyid Ali Sistani shugaban mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Iraki ya bukaci mutane da su guji wuce gona da iri kan Ahlul Baiti (AS).

Ya sanar da wannan bukatar ne a matsayin martani ga wata tambaya da aka yi kan wasu lamurra da suka shafi Imam Ali (a.s.) da Imam Husaini (a.s.)

Ayatullah Sistani ya sha rokon masu magana da mawaka da masu yabon Ahlul Baiti (A.S) da su guji wuce gona da iri a harkokin addini.

از غلو درباره اهل بیت (ع) خودداری شود

 

4165160

 

captcha